Bayan sama da wata daya da sace su, gwamnatin tarrayya tayi nasarar kubutar da wasu daga cikin yan matan da mayakan boko haram suka sace.

Kamar yadda rahotannin suka bayyana yan matan sun dawo ga iyayen su bayan yarjejeniya da jami'an gwamnati suka yi  safiyar yau.

Sai dai babu takamammen bayani kan adadin su ko wata lahani a lafiyar su.

Labari yazo mana cewa jami'an tsaro sun hana manema labarai damar daukar rahoton yadda musayyan ya auku tsakanin yan ta'adda da jami'an gwamnati.

Daya daga cikin iyayen sun sanar ma wakilin channelstv cewa diyar su ta dawo gida gare su.

Zamu fitar da sauran bayanai kan lamarin nan ba da jimawa.