Pulse.ng logo
Go

Zanga-zanga Yan shi'a sun kai koken su gidan Bola Tinubu dake Legas

Mabiyan sun gudanar da zanga-zanga ne a ranar laraba 9 ga watan Mayu har gidan tsohon gwamnan Legas dake nan unguwar Ikoyi.

  • Published:
Yan shi'a sun gudanar da zanga-zanga a har gidan Bola Tinubu dake jihar Legas play

Yan shi'a sun gudanar da zanga-zanga a har gidan Bola Tinubu dake jihar Legas

(BBC hausa)

Dandazon mabiyan kungiyar 'Yan uwa musulmai sun kai koken su gidan jigon jam'iyyar APC, Bola Tinubu dake jihar Legas.

Mabiyan sun gudanar da zanga-zanga ne a ranar laraba 9 ga watan Mayu har gidan tsohon gwamnan Legas dake nan unguwar Ikoyi.

Yan shi'a sun gudanar da zanga-zanga a jihar Legas play

Yan shi'a sun gudanar da zanga-zanga a jihar Legas

(BBC Hausa)

 

Kamar yadda BBC ta ruwaito, sun mika masa takarda koke domin ya isar ma shugaba Muhammadu Buhari kan jagoran su wanda ake cigaba da tsare.

Sun kuma bukaci Tinubu da ya sa baki wajen ganin an saki Ibrahim El-zakzaky.

Wannan ya biyo bayan arangama da suka yi da rundunar yan sanda a garin Abuja inda aka kama mabiyan kungiyar da dama.

Yan shi'a sun kai koken su gidan Bola Tinubu dake jihar Legas play

Yan shi'a sun kai koken su gidan Bola Tinubu dake jihar Legas

(BBC hausa)

 

Sakamakon hargitsin da ya faru tsakanin su, a wata takardar sanarwa da kakakin rundunar DSP  Anjuguri Manzah ya fitar, ya bayyana cewa ba'a rasa rai sakamakom tarzoman da ya faru domin jami'an sun nuna kwarewarsu wajen shawo kan rikicin.

Sai dai ya kara da cewa jami'a 22 suka jikkata sakamakon hargitsin kuma an gano wasu kanan makamai tare da wadanda suka kama.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement