ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Yan sanda sun kama wadanda ake zargi da watsawa dalibar jami'ar Maiduguri ruwan batiri a fuska

Wanda ake zargi ya aika hakan ne saboda iyayenta sun hana shi aurenta kasancewa suna soyaya da juna

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Borno, Mista Damian Chukwu ya tabbatar da hakan a yayin da yake yi wa manema labarai karin haske a garin Maiduguri.

Fatima Usman wacce take kwanciyar jinya a asibitin koyo na jami'a Maiduguri, sakamakon ruwan batiri da aka zuba mata a fuska da wasu sassa na jikin a daren ranar 16 ga watan Maris.

A bisa labarin da jaridar RARIYA ta ruwaito kwamishinan 'yan sanda ya kara da cewa jami'an 'yan sanda na SARS ne suka kama wanda ake zargin a Kano.

Sannan kuma ya kara da cewa jami'an tsaron sun kuma kama wani mai suna Muhammad Babangida wanda ya taimakawa Faisal suka watsawa Fatima guban.

ADVERTISEMENT

Bincike ya nuna cewa Faisal ya yanke hukuncin watsawa Fatima guban ne saboda iyayenta sun hana shi aurenta.

Kwamishinan yana mai cewa "Binciken mu ya nuna mana cewa Fatima da wanda ake zargin sun sha haduwa a sirrance.

“A ranar da lamarin zai auku sun shirya za su hadu a wani otal dake yankin Galadima a garin Maiduguri, inda a yayin da suke cikin daki sai abokin nasa Muhammad Babangida ya zo ya same su.

"Babangida shine wanda ya watsawa Fatima guban imda wajen watsawar ne guban ya samu Faisal a hannu.

"Haka kuma mun gano cewa wanda ake zargin ya sha alwashin cewa sai ya dauki mataki akan Fatima kasancewar iyayen ta sun hana shi aurenta".

ADVERTISEMENT

Ya ce an saka ta a babur mai kafa uku ne domin a yi zaton cewa a cikin babur din ne aka watsa mata guban.

Daga karshe kwamishinan ya rufe da cewa wadanda ake zargin sun amsa laifin su, kuma nan ba da dadewa ba  za'a gurfanar dasu gaban kotu domin saurara hukuncin laifin su.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

Recommended articles

Here's everything to know about being a virgin on your wedding night

Here's everything to know about being a virgin on your wedding night

7 do's and don’ts of the Holy month of Ramadan

7 do's and don’ts of the Holy month of Ramadan

Top 5 sweetest celebrity mother-child relationships that stand out for us

Top 5 sweetest celebrity mother-child relationships that stand out for us

International Women's Day: 5 Nigerian female celebrities championing women’s rights

International Women's Day: 5 Nigerian female celebrities championing women’s rights

Top 5 female directors in Nollywood

Top 5 female directors in Nollywood

6 things that will break a Muslim's fast during Ramadan

6 things that will break a Muslim's fast during Ramadan

5 benefits of fasting during Ramadan

5 benefits of fasting during Ramadan

5 reasons Easter was more fun when we were children

5 reasons Easter was more fun when we were children

Dos and don’ts of supporting Muslims during Ramadan

Dos and don’ts of supporting Muslims during Ramadan

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT