Pulse.ng logo
Go

A jihar Katsina Yan sanda sun kama masu satar mutane

Masu garkuwan suna cikin tawagar masu sata da suka addabi al'ummar karamar hukumar Kafur da Danja

  • Published:
CJN directs Magistrates to inspect police stations monthly play

The police in Nigeria is everything but a friend

(The Nation)

Rundunar yan sandan jihar Katsina ta kama wasu da ake zargi masu garkuwa da mutane ne su takwas.

Kakakin rundunar DSP Gambo Isa ya sanar da hakan a wata takardar sanarwa da ya fitar wa manema labarai ranar litinin 16 ga wata a garin Katsina.

Masu garkuwan da aka kama sun hada da; Joshua Yohanna, mai shekaru 22; Musa Ibrahim, mai shekaru  25; Nafiu Umar, mai shekaru 32; da Kabir Lawal, mai shekaru 28. An kama su a karamar hukumar Kafur na jihar.

Kakakin ya bayyana cewa barayin sunyi barazanar sace wani Haruna Bello da Nuhu Yusuf dake garin Gozaki idan har basu kudin fansa na naira miliyan uku (N3M).

Kamar yadda ya sanar,  bayan biyan N300,000 da suka yi, wadanda barayin suka tasa gaba suka kawo kara ofishin yan sanda, wanda ta hakan aka gudanar da bincike har aka kama su.

Yace suna daga cikin barayin da suka addabi karamar hukumar Kafur da Dan jihar.

An kuma kama wasu barayi su hudu, Mubarak Babangida, mai shekaru 21; Abubakar Lawal, mai shekaru 19; Aliyu Lawal, mai shekaru 22;da Nura Abdulhamid, mai shekaru 22.

Yace an kama su sanya da rigunan mata yayin da suke kokarin sace wani yaro dan shekara hudu.

Kakakin ya kara da cewa za'a gurfanar dasu gaban kuliya bayan kammala bincike.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.