Pulse.ng logo
Go

A jihar Kebbi Yan sanda sun kama masu garkuwa da mutane 4

An kama barayin ne a titin Koko-base zuwa Fakai yayin da dakarun yan sanda ke sintiri. Yace an gano naira dubu dari takwas a tare dasu (N800,000)

  • Published:
Police round-up three suspected child trafficking syndicates in Abia play

Nigerian police

(The News (Nigeria))

Rundunar yan sanda ta jihar kebbi ta kama wasu da ake zargin cewa masu garkuwa da mutane ne su hudu a karamar hukumar Koko-base.

Mai magana da yawun rundunar na jihar Kebbi DSP Mustapha Sulaiman ya tabbatar da labarin inda ya sanar ma manema labarai a garin Birnin kebbi ranar lahadi 15 ga wata cewa an kama barayin ne a titin Koko-base zuwa Fakai yayin da dakarun yan sanda ke sintiri. Yace an gano naira dubu dari takwas a tare dasu (N800,000).

An kama wadanda ake zargin, Muhammadu Mani da Muhammadu Muhammadu da Umar Muhammadu da Abdulkarim Isiya hanyar su na zuwa karamar hukumar Zuru.

Kamar yadda NAN ta fitar, barayin sun kama wani shugaban wata gundumar yan fulani na Koko-base mai suna Alhaji Aliyu Dikko, wanda har sun amshi naira dubu dari uku daga cikin miliyan uku da suka bakaci iyalen sa da biya kafin su sake shi.

Hakazalika masu garkuwan sun kuma amshi naira dubu dari biyar daga iyalen wani da suka sace kafin dubun su ya cika har suka shiga hannun yan sanda.

Kamar yadda DSP Mustapha Sulaiman ya sanar, za'a gurfanar dasu gaban kotu domin sauraron hukuncin laifin su.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.