Pulse.ng logo
Go

Ziyarar Buhari zuwa Ingila Kalli yadda yan Nijeriya dake Landan suka gudanar da zanga-zangar kin jini yayin da shugaban Buhari ya isa babban birnin

Masu zanga-zangar sun gudanar da hakan ne don nuna facin ran kan kudirin da shugaban ya bayyanar na sake tsayawa takara a zaben 2019

  • Published:

Wasu yan Nijeriya mazaunin kasar Ingila sun gudanar da zanga-zangar kin jini a birnin Landan babban birnin kasar.

Lamarin ya faru ne ranar talata 10 ga watan Afrilu yayin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sauka kasar domin kai ziyarar aiki.

Masu zanga-zangar sun gudanar da hakan ne don nuna facin ran kan kudirin da shugaban ya bayyanar na sake tsayawa takara a zaben 2019.

Sai fadar shugaban kasa tayi fashin baki kan lamarin inda ta dangata faruwar hakan bisa aikin yan adawa da makiyin gwamnatin shugaban.

A wata sanarwa da ya fitar, kakakin shugaban kasa, Garba Shehu ya ce tarzoman ba zai hana shugaban cimma manufar ziyarar da ya kai Birtaniya ba inda ya nuna cewa mafi yawan masu zanga zangar, anyi hayarsu ne.

Ziyarar shugaba Buhari zuwa kasar Ingila

A ziyarar da shugaban ya kai kasar nahiyar turai, zai tattauna da firayi ministan Ingila wato Theresa May kan dangantaka dake tsakanin kasar Nijeriya da Ingila.

Shugaban zai kuma tattauna da shugaban kamfanin Dutch royal plc mista Ben van Beurden da kamfanin Shell da makamantan su kan matakin zuba jari a masana'antar mai na kasar Nijeriya.

Bugu da kari, shugaba Buhari zai tattauna da Archbishop na Centebury Justin Welby, wanda yake abokin shine domin inganta zamantakewa tsakanin mabiya addinai daban-daban.

Daga karshe shugaban zai gana da wasu jami'ai na Ingila da kuma yan Nijeriya mazaunin kasar.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.