ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Nijeriya bata yi nasar ba sai yan wasan ta sun birge da irin kwallayen da suka saka a raga

Wasan sada zumunci wanda aka buga a filin wasa na Godswill Akpabio dake garin Uyol, ya tashi 3-2 a madadin Athletico.

Tawagar yan wasan na biyu na super eagle sun buga wasa da zakarun kofin Europa league a daren ranar talata 22 ga watan Mayu.

Wasan sada zumunci wanda aka buga a filin wasa na Godswill Akpabio dake garin Uyol, ya tashi 3-2 a madadin Athletico.

Wasan wanda shahararrun yan wasan kungiyar zakarun Europa league ya kayatar sosai ganin yadda matasan yan wasan Super eagles suka dirje domin birge yan kallo.

Nijeriya ta fara saka kwalo a raga da taimakon Kelechi Nwakali sai dai kuma Angel Correa ya barke inda wasan ya  tashi 1-1 a rukuni na farko.

ADVERTISEMENT

Fernando Torres ya dora Athletico kan gaba bayan dawowar rukuni na biyu. Dan wasan Super eagles, Usman Muhammed ya barke cin da Torres yayi inda saka kwallo a ragar golan Madrid bayan yayi raga-raga da mai tsaron bayan ta.

Sai dai kwallon Muhammed bai yi ta'asiri ba wajen taimakawa Nijeriya na tashi da kunnen doki domin dab da tashin wasan Borga Garcia Moreno ya dora Madrid tafarkin nasara inda daga bisani aka tashi 3-2.

A kafafen sada zumunta da sauran kafofin watsa labarai, yan nijeriya sun nuna gamsuwar su da irin kokarin da matasan Nijeriya suke a wasan.

Muhimman abubuwan da ya dauki hankali shine bisa gwaninta da Nwakali da Muhammed suka nuna yayin saka kwallo a ragar kungiyar kasar Andalus.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT