Daya daga cikin yan matan Chibok ta kubuta daga hannun boko haram

Mataimakin kakakin rundunar 'Operation lafiya dole' kanal Onyeama Nwachukwu ya sanar da wannan labari a wata takarda da ya fitar ma jama'a

Yarinyar mai suna Salomi Pagu ta samu nasarar fita daga inuwar yan boko haram sanadiyar tafiyar bazata da sojojin suka yi zuwa garin Pulka dake nan jihar Borno a ranar alhamis 4 ga watan Janairu 2018.

A bisa takardar sanarwa da mataimain kakakin rundunar kuma babban kwamanda na Operation Lafiya dole kanal Onyema Nwachukwu, ya fitar cewa an tsiratar da Salomi tare da wata mai suna Jamila Adam mai kimanin shekara 14 tare da dan jariri.

Nwachukwu ya kara da cewa har yanzu matan suna nan lafiya a hannun dakarun sojoji kuma suna ta karban maganin domin kula da yanayin lafiyar su.

Kama yan matan Chibok

Cikin watan Afrilu na 2014 ne yan ta'adar Boko haram suka far ma makarantar sekandare ta mata dake nan garin Chibok inda har suka yi garkuwa da yan mata 276 dalibai.

Bayan arangama da kai kawo da dakarun sojoji suka yi da yan ta'adar an samu an kubitar da wasu da dama daga hannun su.

Har illa yau dai akwai sauran yan mata 112 a hannun yan ta'adar.

Wannan nasarar ya fito kwana biyu bayan fitar sakon bidiyo da kungiyar boko haram ta sakar inda jagoran kungiyar Abubakar Shekau ke sanar cewa suna nan lafiya.

Jagoran boko haram ya kara da cewa babu abun da jami'an tsaro zasu iya tsinana masu kuma babu abun da zasu samu daga gare su domin suna cikin inuwar Allah. Bugu da kari yana mai sanar ma jami'an  tsaro cewa babu mutumin da zai koma ga Allah sai dai idan har kwanan sa ta kare.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

Recommended articles

Top 5 transfer hijacks in Premier League history

Top 5 transfer hijacks in Premier League history

Regina Daniels and hubby welcome 2nd child

Regina Daniels and hubby welcome 2nd child

PDP in disarray as crisis over Atiku’s selection of Okowa worsens

PDP in disarray as crisis over Atiku’s selection of Okowa worsens

BREAKING: Bandits kidnap Chinese nationals, kill 6 soldiers, 7 cops

BREAKING: Bandits kidnap Chinese nationals, kill 6 soldiers, 7 cops

I’m lonely – Physically challenged 56-year-old virgin regrets rejecting men (video)

"I’m lonely" – Physically challenged 56-year-old virgin regrets rejecting men (video)

For men: Here're 4 ways to tell if your partner is faking orgasm

For men: Here're 4 ways to tell if your partner is faking orgasm

Ortom calls out PDP for betraying Wike

Ortom calls out PDP for betraying Wike

Inside the most expensive school in Ghana where kindergarten costs GHc176K a year

Inside the most expensive school in Ghana where kindergarten costs GHc176K a year

When and where to watch Super Eagles of Nigeria vs São Tomé and Príncipe

When and where to watch Super Eagles of Nigeria vs São Tomé and Príncipe