Pulse.ng logo
Go

Al'adar hausa har kasar Sin Kalli yadda yan kasar China ke kwaikwayon rawar wakar shirin Rariya ta Rahama Sadau

A cikin bidiyon wanda jarumar ta saka a shafin ta ta Instagram, za'a gan yadda daliban jami'ar Shenyeng ke tika rawa ga wakar shirin RARIYA

  • Published:

Wasu daliban wata jami'ar kasar sin sun nuna soyayar da suke ma wakokin hausa inda  a wata bidiyo dake yawo a kafaafen sada zumunta, za'a gan yadda suke tika rawa ga wakar RARIYA ta shirin fim wanda Jaruma Rahama Sadau ta shirya.

Shirin fim din, shine na farko da fitacciyar jaruma zata shirya da kanta kuma ya samu karbuwa matuka ga dinbim masu bibiyan fina-finan hausa na gida har da yan kasar waje.

Shirin fim wanda ya samu haskawan fitattun manyan jarumai kamar Ali Nuhu da Sadiq Sani Sadiq da Fati Washa da Hafsat Idris da Maryam Booth da sauran su, ya samu lambar yabo na kyuatar City People Awards 2017.

 

Jarumar ta nuna farin cikin ta bisa wannan kokarin da daliban suka yi na yin wakar tare da kwaikwayon rawar da aka taka na wakar cikin shirin.

Daliban jami'ar Shenyeng sun kayatar matuka kuma da alama al'adar kasar hausa ya samu karbuwa a kasar Sin.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.