Kakakin Majalisar tarayya Yakubu Dogara yace zai sake tsayawa takara duk da cewa wasu na son suyi masa ritaya.

Ya kara da cewa ba zai daina tsayawa takara ba sai ya kammala ayyukan cigaba da yake yi ma kasa.

A cikin sakon da ya wallafa a shafin sa na Tuwita, jagoran majalisar wakilan tarayya yace zai tsaya takara bayan amincewar al'ummar mazabar sa.

Bugu da kari yace zai tsaya takara don ya karya mutanen dake neman yi masa ritaya.

Da alama ya mayar da da raddin ne ga gwamnan jihar Bauchi da Bola Tinubu wandanda ake ganin sun samu rashin jituwa bayan yayi nasarar zama kakakin majalisa.

Yakubu Dogara yana wakiltar al'ummar yankin Bogoro/Dass/Tafawa Balewa na jihar Bauchi ya shiga zauren majalisar tarayya tun cikin shekarar 2007.

Duk da cewa ya jaddada cewa zai sake tsayawa takara a zaben 2019, kakakin bai sanar da jam'iyar da zai fito takara karkashin ta.