Dakarun bataliya 145 na rundunar sojojin Nijeriya sunyi musayyar wuta da mayakan kungiyar taadan Boko Haram yayin da mayakan suka kawo farmaki shingen sojojin.

A labarin da kakakin rundunar sojojin Nijeriya Birgediya janar Texas Chukwu ya fitar, lamarin ya faru a yammacin ranar Laraba 12 ga wata.

Kakakin ya sanar da haka a shafin sa na Facebook tare da sanar cewa sojoji sun samu nasarar fatattaki yan ta'addan.

Lamarin dai ya faru ne a shingen sojojin dake nan garin Damasak na jihar Borno a daidai karfe 6 na yamma.

Barin wutar da sojojin suka yi da yan ta'addar ya biyo bayan kwana biyu da ministan yada labarai ya sanar cewa gwamnatin shugaba Buhari tayi nasarar rage illar da aika-aikar yan ta'ada a kasar.

Lai Mohammed ya fadi hakan ne a wajen taro kan batun  tsaro da aka gudanar a garin Gusau babban birnin jihar Zamfara ranar litinin 10 ga watan Satumba