Pulse.ng logo
Go

Toh fa! Ya shigar da kara kotu bayan abokin shi ya nemi ya kwace masa mata

Yusuf ya ce kwace ce ta karfi da yaji Mustapha yake so yayi masa, sannan ya na rokon kotu ta shiga tsakanin su wajen  raba su ta dawo masa da matar sa.

  • Published:
Hoton wani zaman kotun sharia a arewacin Nijeriya play

Hoton wani zaman kotun sharia a arewacin Nijeriya

(British council Nigeria)

Wani magidanci dake zama a jihar kaduna ya shigar da kara kotu kan zargin da yake ma abokin sa na neman kwace masa mata.

Kotu dake gudanar da zaman ta a Magajin Gari dake garin Kaduna ta gurfanar da wani mutumi dake kokarin yi wa abokin sa kwace.

Yusuf Sadi  ya shigar da karar a kotu inda ya bayyana cewa Abubakar Mustapha ya fara bibiyar matarsa mai suna Nusaiba bayan ta tafi gidan su dake Kafanchan yin wankan jego.

Yana mai cewa ”Tun da mata ta ta tafi gidan su wanka har yau ta ki dawo wa gida".

”Sannan a lokacin da na je duba ta da sabon jariri Mustapha ya yi barazanar la’anta ni saboda na bita har cikin dakin sa da taho garin.

Yusuf ya ce kwace ce ta karfi da yaji Mustapha yake so yayi masa, sannan ya na rokon kotu ta shiga tsakanin su wajen  raba su ta dawo masa da matar sa.

Sai dai shi wanda ake zargi ya karya ta karar da aka shigar a kansa.  Kotu ta mika shi ga ‘yan sanda domin cigaba da bincike kafin a kara sauraron karar.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.