Tsokacin yan kasa bayan wasan Nijeriya da Argentina

Mutane da dama sunyi tsokaci game da wasan. A kafafen sada zumunta da na watsa labarai, al'ummar Nijeriya sun jinjina ma yan wasan tawagar super eagles bisa jajircewa da birgewa da suka yi a gasar bana.

Shaharrarren dan wasa, Lionel Messi ya fara zura kwallo a raga kafin Victor Moses na Nijeriya ya rama. Daf da a tash, Marcos Rojo, ya zurra matabbaciya a ragar Francis Ezoho.

Lamarin dai ya bai yi ma jama'a dadi domin sakamakon wasan ya sanya Nijeriya zata fita gasar bana.

Wasu na ganin, mai jagorantar da wasa, ya nuna son kai wajen hana Nijeriya fenerti da makamantar haka a wasan.

Hakazalika wasu kuma sun nuna bacin ran su ga yan wasa, Odion Ighalo da Kelechi Iheanacho, sakamakon damar da suka samu amma suka baras.

Babban direkta a masana'antar kannywood, Falalu Dorayi, ya rubuta " Kwallo ba tai dadi ba, wannan Ighalo sai yaci...."

Cikin jama'a masu fashin baki dangane da wasan akwai jarumai da dama da masu hannu da shuni a fannoni daban-daban.

Shahararren mawaki, Banky W, wanda ya garzaya har filin da aka buga wasan domin mara ma yan wasan Nijeriya baya, ya jinjina masu duk da rashin goyon baya da suka samu a filin wasa.

Sakamakon wasan dai ya saka Nijeriya cikin jerin sauran kasashen Afrika uku dake shirin dawowa gida bayan sunyi rashin nasara na tsallakewa zuwa zagaye na biyu a gasar.

A tarihi dai, sau biyar kenan Nijeriya ke haduwa da Argentina a gasar kofin duniya kuma a duk lokatan da suka hadu Argentina ta samu galaba kan kasar nahiyar Afrika.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

Recommended articles

Beatrice and Boma face off in new BBNaija Reunion teaser

Beatrice and Boma face off in new BBNaija Reunion teaser

IPOB kills woman, 4 kids, 6 other northerners in Anambra

IPOB kills woman, 4 kids, 6 other northerners in Anambra

Why is the dollar shortage crisis in Africa getting worse by the day?

Why is the dollar shortage crisis in Africa getting worse by the day?

Top 10 happiest countries in Africa in 2022

Top 10 happiest countries in Africa in 2022

Bolton's new 'Jay-Jay Okocha' wants to represent Nigeria ahead of England

Bolton's new 'Jay-Jay Okocha' wants to represent Nigeria ahead of England

Arsenal suffer a blow as Osimhen makes his transfer decision

Arsenal suffer a blow as Osimhen makes his transfer decision

Rubber producers present life crocodile to Obasanjo, say they can’t give him money

Rubber producers present life crocodile to Obasanjo, say they can’t give him money

10 African countries with the largest foreign exchange reserves

10 African countries with the largest foreign exchange reserves

Here are the 5 worst cities to live in Africa, according to Economist Intelligence Unit report

Here are the 5 worst cities to live in Africa, according to Economist Intelligence Unit report