ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Wani ma'aikacin JAMB ya batar da miliyan 23 na hukumar, ya daura laifin ga wata mummunar dalili

Ya shaida hakan ne yayin da tawagar shugaban hukumar na kasa ta ziyarci ofishin hukumar don gudanar da bincike domin gano masu badakala da kudin hukumar.

Ya shaida hakan ne yayin da tawagar shugaban hukumar na kasa ta ziyarci ofishin hukumar don gudanar da bincike a domin gano masu badakala da kudin hukumar.

Wannan lamarin ya faru kwana biyu bayan labarin wata ma'aikaciyar hukumar ta sanar cewa maciji ya hadiye miliyan 36 na hukumar a ofishin ta.

A cewar ta mai aikin gidan ta tare da abokiyar aikin ta Joan Asem suka hada hannun wajen wawushe kudin ta hanyar tsubbu daga asusun ajiya na hukumar.

Yayin da yake bada shaidar yadda kudin suka bace, Tanko yace lamarin ya faru ne cikin shekara 2016 kuma a daidai lokacin yana fama da wata rashin lafiya. Daga bisani yace ba da sanin shin aka sanya katutukar shiga a motar shi.

ADVERTISEMENT

Shi dai shugaban hukumar na kasa Ishaq Oloyede ya karyata zargin inda ya sanar cewa katin da shi Tanko ya bada shaidar cewa ta kone ya gano ta hanyar na'ura cewa anyi amfani dasu ne a nan jihar Nasarawa.

Hukumar tace zata gurfanar da shi da dayan matar ga hukumar yan sanda domin cigaba da bincike kan zargin da ake masu na yi ma kudaden hukumar zagon kasa.

Hukumar JAMB ta fara shirin gyara fuska ga ma'aikatan ta domin gano masu yi ma arzikin gwamnati ta hanya hukumar amare da tare da an sani

Wannan yunkurin ana dangana ta da hadin gwiwar da hukumar tayi da hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa wato EFCC.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT