ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Arewa zata samar da shugaban kasa a zaben 2019

“Muna son mu jaddada cewa arewa baza ta taba yarda mulki ya koma kudu”, inji kungiyar.

APC Presidential candidate, Muhammadu Buhari campaigns in Borno State. 

ƙungiyar matasa na arewa sun bayyana cewa shugaban kasan naijeriya zai kasance daga arewa a zaben 2019.

Shugaban ƙungiyar Comrade Elliot Afiyo, ya bayyana ma manema labarai cewa; “ba zamu taba yarda shugabancin kasar ta koma kudu a zaben 2019”

“Ina son in jaddada cewa arewa baza ta taba yarda mulki ya fita daga yankin a zaben 2019”Ariyo yace

“Duk da cewa mun amince da hanyoyin neman zaman lafiya da ake yi, baza taba yarda shugabanci ya bar yankin mu ba. Mun koyi darasi a zaben 2011 da 2015.” ya kara.

ADVERTISEMENT

A kwanan baya kungiyar ta zayyanar da wasu yan takara daga yankin.

Sun kunshi, shugaban majalisar datawa Bukola Saraki, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, tsohon gwamnan jihar jigawa Sule Lamido, gwamnan jihar kaduna Nasir el-rufar da gwamnonin jihar Gombe, Zamfara, sokoto da Borno.

Sauran sun hada da senata Bala Muhammed, Rabiu Musa Kwankwaso, Ali Modu Sheriff da Alh Tanimu Turaki.

A wani taro da ƙungiyar tayi a kaduna, sun kaddamar da takarar Atiku Abubakar, Senata Bala Muhammed da Alh Tanimu Turaki.

A halin yanzu, shugaban jam’iyar APC John Oyegun ya bayyana cewa jam’iyar zata ba shugaba Buhari tikitin takarar zaben 2019.

ADVERTISEMENT

Oyegun ya kara da cewa gwamnatin Buhari na iya bakin kokari don tafiyar da alamura yanda ya kamata inda ya kara da cewa yakin da gwamnatin keyi wajen magance cin hanci da rashawa yana cikin tsarin jam’iyar.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT