ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Tsohon gwamna ya amshi horo mai tsanani hannun EFCC

An tuhume shi ne bisa zargin yin rashawa da naira biliyan N10 na kudin jihar Filato yayin da yake gwamna

An tuhume shi ne bisa zargin yin rashawa da naira biliyan N10 na kudin jihar Filato yayin da yake gwamna.

Tsohon gwamnan wanda a yanzu dan majalisar dattawa ne mai wakiltar yankin arewacin jihar ya shiga ofishin hukumar tun karfe 10 na safe har wajen karfe 8 na dare kana ya samu damar fita daga ofishin su.

Wani jami'in hukumar EFCC ya shaida ma wakilin jaridar Punch cewa Dan majalisar ya amsa kiran da hukumar tayi  mai na ya gabatar da kanasa ofishin su ranar talata. Ya kara da cewa tsohon gwamnan zai kara ziyartar  ofishin hukumar ranar laraba domin cigaba daga inda aka tsaya.

Rahotannin sun nuna cewa kara da dama aka kai game da badakalar da tsohon gwamnan wanda yayi mulki tun daga 2007 zuwa 2015 yayi.

ADVERTISEMENT

Cikin wadanda suka kai karar shi akwai gwamnan jihar na yanzu Simon Lalong.

Gwamna Lalong yana zargin Jang da wawushe tallafin kudi ta musamman (Naira biliyan N2) wanda babban banki kasa ta baiwa jihar Filato a zamanin mulkin shi domin gabatar da shirin kananan kasuwanci.

Banda wannan laifin ana zargin tsohon gwamnan da aikata makamancin haka a ma'aikata da dama na jihar tare da sauya alkiblar wasu kudade zuwa wasu kamfanoni masu zaman kansu.

Jang ya musanta wannan zargin da ake masa har ma ya kara da cewa ya jagorancin jihar cikin adalci.

Hadimin shi mista Olivia Dazyam ya shaida manema labarai cewa dan najalisar ya amsa kiran EFCC ne domin ya wanke kansa bisa zargin da ake mashi.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT