ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Tsohon Gwamna yayi shelar tsayawa takarar shugaban jam'iyar APC

Ya Bayyanar da annjiyar sa na tsayawa takarar shugabancin jam'iya a wata taro ta musamman da aka shirya a garin Abuja

Ya dau alwashin hada kan jami'o'in gwamnatin kama daga bangaren shugabanci da majalisu.

Yayin da ya bayyanar da anniyar sa ga bainar jama'a a garin Abuja ranar alhamis 10 ga watan Mayu, Adam Oshiomhole yace zai tabbatar da samun nasara a ko da yaushe idan an zabe shi a matsayin shugaba.

Ya kara da cewa zai yi amfani da kwarewarsa a zamanin da yayi shugabancin kungiyar kwadago na NLC wajen shawo kan yayan jam'iyar.

Tsohon gwamna yana mai tabbatar da ma shugaban kasa da gwamnoni tare da yan majalisa cewa, ya na cike da kwarewa wanda cancanci ya zama jagoran jam'iyar mai ci.

ADVERTISEMENT

Daga karshe, yayi ma jiga-jigai da iyayen jam'iyar bisa rawar da suka taka wajen raya jam'iyar da irin nasarori da suka samu.

Taron kaddamar da shelar takarar sa ya samu halartar gwamnan jihar Edo da yan majalisun jihar karkashin jagorancin kakakin majalisa tare da tsohon gwamnan jihar Bayelsa da Sanata Ita Enang da sauran su.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT