Pulse.ng logo
Go

Joshua Dariye Kotu ta daure tsohon gwamna a kurkuku na tsawon shekara 14

An kama shi da laifin canza arkallar kudin asusun gyara muhalli da hallitu wato Ecological Funds

  • Published:
Kotu ta daure tsohon gwamna a kurkuku na tsawon shekara 14 play

Tsohon gwamna ya samu hukuncin dauri na shekara 14

(lindaikeji)

Kotun tarayya dake babban birnin tarayya ta bada hukuncin daurin shekaru 14 a gidan kaso gha tsohon gwamnan jihar Filato.

Joshua Dariye ya samu hukuncin ne bayan ga karar da hukumar hana cin hanci da rashawa ta EFCC ta shigar wanda take zargin shi da wawure kudin jama'a sanda yake gwamna.

A zaman kotu da aka yi ranar talata 12 ga wata, an kama Dariye da aikata laifufuka 15 daga cikin 23 da aka shigar a kansa.

Bayan ga haka an kuma kama shi da canza arkalar naira biliyan daya na daga cikin asusun gyara muhalli.

Kamar yadda aka bayyana a kotu, tsohon gwamnan wanda yake dan majalisar dattawa yanzu ya sauya manufar kudin ne ta hanyar wata kamfani mallakar shi mai suna Ebenezer Reitner Ventures.

Mai sharia Adebukola Banjoko ta zantar da hukunci bayan shafe sa'o'i 5 ana muhawara a kotu.

Shi dai tsohon gwamna ya shafe shekaru 10 ana sauraron karar zargin da EFCC ta shigar a kanshi, sai yanzu shari'a ta tabbatar da laifin shi.

Tare dashi, shima dan shi Nanle Dariye na fuskantar tuhuma kan zargin laifin almumdahana.

Hukuncin dauri da Joshua Dariye ya biyo bayan wanda aka yi ma tsohon gwamnan jihar Taraba Rebren Jolly Nyame.

Bayan shafe sama da shekaru 10 ana sauraron karar da aka shigar a kansa, shima tsohon gwamnan ya samu hukuncin dauri na tsawon shekara 14 kan laifin wawure kudin jama'a sanda yake kan karagar mulkin jihar.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement