Inda nine Jonathan a zaben 2015 da na tada riƙici a ƙasar - inji wani Gwamna

Gwamnan jihar Ribas Nyesom Wike yace Goodluck Jonathan ya fadi a zaben 2015 kasancewa shi mutum ne mai kyakyawan dabi’a

Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas yace tsohon shugaban kasa ya fadi a zaben 2015 kasancewa shi mutum ne mai tausayi.

Gwamnan wanda yake jam’iya daya da tsohon shugaban ƙasa na PDP yace Jonathan ya fadi zaben ta hanyar da bai dace ba.

Wike ya sanar cewa da ya gabatar da wani tsarin yin kamfe inda yana cikin tawagar neman kuri’a na tsohon shugaban ƙasa a zaben 2015.

Bayan zaben wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya lashe an samu labari cewa wasu magoya bayan jam’iyar APC sun jefa ma tawagar Jonathan duwatsu yayin da suka shigo arewa domin yin kamfe.

Da wannan gwamnan yake cewa inda shine wanda alamarin ya faru dashi da anyi ba dai-dai ba a kasar domin ba zai lamunta da irin wannan cin fuska indai shine shugaban ƙasa.

Ya kara da cewa sai duk abun da zai faru ya faru amma shi dai sai aikata abun da ran shi inda shine aka jefa ma duwatsu alhalin yana shugaban ƙasa.

A wata hira ta musamman da yayi da mujallar ‘The interview’ gwamnan yana zargin da sa hannun masu ruwa da tsaki a arewa aka ci zarafin Jonathan ciki ma har da wasu yan jam’iyar PDP.

Bisa da lamarin da ya faru yayin da ake kirgen zaben 2015 tsakanin shugaban hukumar zabe farfesa Attahiru Jega da Goodswill Orubebe, Wike yace shima dai da ya aikata irin abun da Orubebe ya aikata domin shima ba zai yarda ayi magudi a idon sa.

A karshe Wike yayi kira ga yan Nijeriya cewa za'a tada kura a ƙasar indai jam’iyar adawa na APC suka nema suyi magudi a jihar shi a zaben shugaban ƙasa na 2019.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

Recommended articles

The history of the Ojuelegba area in Lagos

The history of the Ojuelegba area in Lagos

Nollywood veteran actor Kenneth Aguba reportedly homeless

Nollywood veteran actor Kenneth Aguba reportedly homeless

Clubless Super Eagles star Kelechi Nwakali surprisingly rejects ₦9.9million salary

Clubless Super Eagles star Kelechi Nwakali surprisingly rejects ₦9.9million salary

2023: Why the Obidient movement is a useless one – Asari Dokubo

2023: Why the Obidient movement is a useless one – Asari Dokubo

Here are 5 things you must do immediately after you have s*x

Here are 5 things you must do immediately after you have s*x

Burna Boy reveals Toni Braxton gets 60% royalty from his song 'Last Last'

Burna Boy reveals Toni Braxton gets 60% royalty from his song 'Last Last'

Mixed reactions as Femi Otedola endorses Tinubu

Mixed reactions as Femi Otedola endorses Tinubu

PDP crisis deepens as Wike reportedly refuses to meet Atiku's emissaries

PDP crisis deepens as Wike reportedly refuses to meet Atiku's emissaries

Here are 5 reasons why your ex is still reaching out to you

Here are 5 reasons why your ex is still reaching out to you