Pulse.ng logo
Go

Toh fa! Gwamna yace rayuwar sa na fuskantar hatsari

Yace an tsige jami'an tsaro dake tsaron shi sanadiyar haka rayuwar shi na fuskantar barazana

  • Published:
President Muhammadu Buhari (right) and the Governor of Anambra State, Willie Obiano play

President Muhammadu Buhari (right) and the Governor of Anambra State, Willie Obiano

(File )

Gwamnan jihar Anambra wanda ke neman zarcewa a zaben da za'a gabatar kwanan nan Willie Obiano yace rayuwar shi na cikin hatsari.

Yace an soke jami'an tsaro dake tsaron shi sanadiyar haka rayuwar shi na fuskantar barazana.

Ya fadi haka a wani taron jama'a da hukumar zabe ta kasa ta gabatar a garin Awka cikin shirin kaddamar da zaben gwamnoni da za'a gabatar nan ba dadewa ba.

"Ina son a dawo mun da masu tsaron baya na cikin gaggawa domin inba haka ba zan tada rigima. Nine gwamnan jihar Anambra kuma ina son duk mukarrabe na su kasance tare dani.

"ba zan lamunta da wannan lamarin kuma duk wanda ke da hannun cikin ta ba zai ji da dadi ba domin mun shirya ma zaben dake gaban mu." gwamnan ya jaddada.

Wannan maganar tasa ya fito bayan an tsige jami'an dake tsaron shi.

Martanin sufeto janar na yan sanda Ibrahim Idris

Babban sufeton yan sanda na kasa ya bayyana dalilin da ya sanya aka tsige jami'an dake tsaron gwamnan.

Idris yace an cire su kasancewa zabe da za'a gabatar a jihar ya gabato.

SUfeton yayi wannan bayanin a garin Awka babban birnin jihar Anambra ranar talata 14 ga watan Nuwamba.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement