Shugaban maaikatar gyaran hanyoyin tarayya reshen jihar Legas, Mista Adedamola Kuti, ya sanar cewa zuwa ranar 26 ga watan Yuli zaa rufe babbar gada ta Third mainland Brideg domin yin gyara.

A taron tattaunawar da aka yi ranar laraba 11 ga watan Yuli a ma'aikatar aiki ta jihar Legas, shugaban ya sanar cewa aikin da za'ayi a gadar zai kai tsawon watanni 27.

Aikin gyaran wanda kamfanin Borini Prono Construction zata gudanar zai hana safara saman gadar kwana uku da farawa domin lura da mataki da za'a bi domin yin gyara mai kyau.

Shugaban ma'aikatar FERMA ta jihar yayi kira ga al'umma da su bada hadin kai tare da bada hakuri bisa takura da aikin zai jawo ga yawan jama'a dake bibiyan gadar.

Ya roke su da suyi amfani da wata hanya daban yayin da aikin ya kankama.

A jawabin sa shima shugaban hukumar kiyaye hadura ta FRSC ta jihar, mistaHyginus Omeje, ya bukaci masu motocin garin da suyi amfani da matocin haya daidai lokacin da aikin ya fara domin rage yawan motoci dake safara wanda ke yawan haifar da cinkoso.

Ya kara da cewa jami'an kula da hanyoyi da kiyaye ka'idojin tuki da motoci zasu bazu a ko wani lungu na jihar domin rage takura da rufe gadar zata haifar.

Takaitaccen tarihin gadar

Gadar Third mainland Bridge wanda aka gina cikin shekarar 1990, mahada ce ga tsakanin garin Legas da tsibirinta (inda yawan ma'aikata da hukumomi suka fi yawa).

Babban gadar wanda kamfanin Julius Berger ta gina ta karkashin mulkin tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Ibrahim Badamasi Babangida ta kai tsawon kilomita 11.8.

Kai ga shekarar 1996 bayan gina ta, ita ce gada mafi tsawo a duk fadin nahiyar Afrika. Gadar 6th October dake Cairo babban birnin kasar Masar ita ce gada mafi tsawo a Afrika tun gina ta a shekarar 1996. Tana da tsawon kilomita 20.5.