Fitacciyar jarumar kannywood, Maryam Booth, tayi farin cikin kammala hidimar kasa ta shirin NYSC.

Tana cikin dubanan matasan Najeriya da suka karba shaidar kammala  shirin na rukinin batch B stream 1 ranar Alha,is 18 ga watan Oktoba.

Ta nuna farin cikin ta kammala shiri a shafin ta na kafafen sada zumunta tare da taya sauran matasa da suka kammala hidimar tare da ita murna.

Suma masoyan ta masu bibiyan shafukan ta sun taya ta murna taya da yi mata fatan alheri.

Gidauniyar Atiku ta baiwa Maryam Booth babban mukami

Gidauniyar Atiku Care Foundation wacce take tallafa wa mara sa galihu ta daukaka mukamin jarumar daga jakadiya zuwa mukamin mataimakin shugaba na  yankin arewa.

Gidauniyar ta sanar da hakan ne ta  hanyar wani sako da ta wallafa a shafin ta na kafafen sadarwa inda ta bayyana cewa matsayin zai fara aiki daga ranar juma'a 21 ga watan Satumba.

Maryam Booth ta shiga sahun sauran abokan aikin ta na masana'antar kannywood dake karkashin wannan gaidauniyar.