Shahararren jarumin Kannywood, Lawan Ahmad, bai gaza nuna farin cikin sa na cika shekaru goma da yin aure kuma dankon soyayar sa ga iyalen sa na cigaba da yin kamari.

Jarumin ya raya zagayowar wannan muhimmin ranar tare da wallafa wasu tayatattun hotuna na shi da iyalen sa a shafin sa na Instagram.

An gan inda jarumi ya haskaka tare da matar sa da yaransu uku da suka samu albarkacin auren su.

Allah ya albarkaci auren su da yara uku, maza biyu Ahmad Lawan Ahmad, Aliyu Lawan Ahmad da yar auta, Fatima Lawan Ahmad.

Cikin sakon da ya fitar, jarumin ya nuna godiyar sa bisa addu'o'i da fatan alheri da ya samu daga dinbim masoyan sa da sauran abokan sana'ar sa.

Lawan Ahmad yana daya daga cikin tsofafin fitatun jarumai dake raya masana'antar fina-finan hausa kai ga wannan zamani.

Bayan fim, Lawan ya nuna sha'awar sa na shiga harkar siyasa. Ya fito takarar majalisar jiha karkashin jam'iyar APC na wakiltar karamar hukumar Danja dake jihar Katsina. Sai dai bai samu nasarar zama gwanin jam'iyar ba.