ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

FIFA ta sauya sakamakon wasan Nijeriya da Algeria tare da hukunta NFF na biyan tara

A wasan wanda aka buga cikin watan Nuwamba, Nijeriya da Algeria sunyi kunnen doki ne inda aka tashi 1-1.

A wasan wanda aka buga cikin watan Nuwamba, Nijeriya da Algeria sunyi kunnen doki ne inda aka tashi 1-1.

FIFA ta fitar da hukuncin ranar talata 12 ga watan Disamba inda take cewa Nijeriya ta sanya dan wasan ta Abdullahi Shehu wanda aka dakatar sanadiyar samun kati biyu a wassanin biyu da suka buga baya cikin wasanin share fage na shiga gasar cin kofin duniya.

A yanzu dai FIFA ta sauya sakamakon wasan zuwa 3-0, nasar ga Algeria kana zata ci hukumar kwallon kafa ta Nijeriya NFF tara bisa ga sakacin da suka yi.

Sai dai wannan sabon sakamakon ba zai kawo cikas ga Super eagles a fagen cin kofin duniya domin ta riga ta samu nasarar tsallake zuwa gasar tun kafin wasan. Amma wannan ya rage makin da Nijeriya ta samu a wassanin share fage daga maki 14 zuwa 13.

ADVERTISEMENT

Nijeriya ta buga wasanni shida, ta samu nasara a wasanni hudu tayi kunnen doki daya hakazalika ta fadi a wasa guda.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT