Hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) ta fitar da sunayen yan takarar gwamna na jihar Sakwato amma sunan Aminu Waziri Tambuwal ba ya ciki.

Wannan ya saba ma mafi yawan tunanin da jama'a keyi na cewa shine dan takarar da jam'iyar PDP ta tsayar bayan da ya fadi zaben fidda gwani na takarar shugaban kasa.

A jadawalin da INEC ta wallafa,  yan takara 34 zasu yi takarar gwamna kuma Mannir Dan'iya shine dan takarar PDP.

Tun asali tsohon kwamishnan shine ya samu tikitin tsayawa takarar gwamna na PDP. Sai dai ana hasashe cewa ya amince da janye ma Tambuwal bayan da gwamnan ya fadi zaben fitar da gwani na takarar shugaban kasa.

Kamar yadda ta sanar, INEC tace jam'iyu nada nan zuwa ranar daya ga watan Disamba su sauya yan takara idan sun bukaci yin hakan.

Har ila yau dai wasu majiyoyi na cewa akwai yiuwa a sauya sunan Tambuwal cikin jadawalin karshe da INEC zata fitar cikin watan Janairu na 2019.

Hakazalika shima shugaban jam'iyar PDP na jihar Sokoto, Alhaji Ibrahim Milgoma, yace har yanzu da sauran lokaci na sauya sunan dan takarar jam'iyar.