Pulse.ng logo
Go

Takarar Buhari Sule Lamido yace PDP ta firgita shugaba Buhari da APC

Ya kara da cewa hankalin APC da ma shugaban zai fi tashi idan har suka gudanar da taron su a jihohin Sokoto, Kebbi da Kaduna kafin ayi uwar taro a Abuja

  • Published:
Why I’m interested in ruling Nigeria — Lamido play

Sule Lamido

(Punch)

Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma jigo a jam'iyar adawa ta PDP Sule Lamido yace jam'iyar sa ta firgata shugaban kasa wajen bayyanar da kudirin sake tsayawa takara.

Hirar shi da BBC, Sule Lamido ya kushe jam'iyar APC inda yace taron da jam'iyar sa tayi a jihohin Jigawa da Katsina wanda ya samu halartar dinbim magoya bayan ta ya tayar da hankalin jam'iyar mai kan mulki.

''Ai taron da aka yi a Jigawa da na Katsina shi ya firgita su, suka ce ranka ya dade gara fa ka zo, domin yadda aka yi taron nan na Jigawa da Katsina, idan ba ka zo ka ce za ka yi takara ba mun shiga uku'' yace.

Ya kara da cewa hankalin APC da ma shugaban zai fi tashi idan har suka gudanar da taron su a jihohin Sokoto, Kebbi da Kaduna kana ayi uwar taro a Abuja.

Sule Lamido ya bi sahun jigon jam'iyar sa Shehu Yusuf wajen kara jaddada cewa anniyar shugaban bata tayar da fargaba a gare su domin a cewar sa PDP ta haifi APC don haka Buhari jikan su ne.

Tsohon ministan ayyukan waje ya kara da cewa Shugaban bai yi nasarar lashe zaben takarar da yayi sau uku sai da taimakon wasu yan PDP irin su Atiku, Kwankwaso, Bukola Saraki, Wamako, Goje da Abdullahi Adamu yayi nasara a karo na hudu.

Daga karshe Sule Lamido yace babu wata damuwa da PDP tayi kan kudirin sa na sake tsayawa takara ganin cewa wadanda suka taimaka mashi wajen samun nasara sun koma gida (PDP).

Neman Takarar Sule Lamido

Tsohonn gwamnan ya bayyana anniyar sa na fitowa takarar kujerar shugaban kasa idan jam'iyar sa ta amince dashi.

Ganawan shi da mabiyan jam'iya PDP na reshin jihar Legas ranar alhamis 22 ga watan Maris, Lamido ya bayyana cewa babban dalilin yunkurin da yake shine don gani ya aiwatar da ayyukan da yan kasa ke bukata kuma ba don dadin mulki ba.

Yace kuddurin sa wajen kawo gyara a kasar da kuma dora ta matsayin da ya kamace ta ya sanya yake neman sauya shugaba Buhari idan Allah ya kai mu zaben 2019.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.