ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Rundunar sojojin Nijeriya zata bada tukwocin N5m ga wanda ya bada labarin mahadar bam

Sojojin sun kara kudin duk a cikin matakin da suka dauka wajen dakiule hare-haren yan ta'ada

Shugaban dakarun Operation lafiya dole, Manjo janar Rogers Nicholas, ya sanar da haka ranar alhamis 21 ga watan Yuni.

Yace wannan yana daga cikin matakai da sojojin Nijeriya suka dauka wajen dakile aika-aikar yan ta'ada da suka addabi al'ummar kasar.

Wannan matakin ya biyo bayan harin da wasu da ake zargin cewa yan ta'ada ne suka kai barikin sojoji dake nan garin Maiduguri ranar laraba 20 ga watan Yuni.

ADVERTISEMENT

Yan ta'adar basu samu damar cinma manufar su ba na tayar da bam da suke dauke dashi a cikin jama'a domin ta tashi gabanin su far ma jama'a.

Bayan ga haka yan ta'adar sun kuma kai hari garin Damboa na jihar Borno a dai dai ranar bikin karamar sallah wanda yayi sanadin mutuwar mutum 43 tare da jikkata wasu da dama.

Harin kunar bakin waken ya faru yayin da al'ummar garin ke shagalin bikin sallah a dai dai karfe goma da minti arba'in da biyar na dare(10:45).

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT