Pulse.ng logo
Go

Yaki da ta'adanci Sojoji sunyi musayyar wuta da mayakan boko haram

Lamarin dai ya faru ne a shingen sojojin dake nan garin Damasak na jihar Borno a daidai karfe 6 na yamma.

  • Published:
Army arrests suspected militia spiritual head play Sojoji suna bakin aiki (PM Nigeria News)

Dakarun bataliya 145 na rundunar sojojin Nijeriya sunyi musayyar wuta da mayakan kungiyar ta'adan Boko Haram yayin da mayakan suka kawo farmaki shingen sojojin.

A labarin da kakakin rundunar sojojin Nijeriya Birgediya janar Texas Chukwu ya fitar, lamarin ya faru a yammacin ranar Laraba 12 ga wata.

Kakakin ya sanar da haka a shafin sa na Facebook tare da sanar cewa sojoji sun samu nasarar fatattaki yan ta'addan.

Lamarin dai ya faru ne a shingen sojojin dake nan garin Damasak na jihar Borno a daidai karfe 6 na yamma.

Barin wutar da sojojin suka yi da yan ta'addar ya biyo bayan kwana biyu da ministan yada labarai ya sanar cewa gwamnatin shugaba Buhari tayi nasarar rage illar da aika-aikar yan ta'ada a kasar.

Lai Mohammed ya fadi hakan ne a wajen taro kan batun  tsaro da aka gudanar a garin Gusau babban birnin jihar Zamfara ranar litinin 10 ga watan Satumba

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement