Hakan ya faru ne yayin da sojojin suka kai hari garin Numan domin safarar yan ta'adda da suka addabi jihar.
Sojoji sun kashe yan ta'ada 10 a garin Numan
Sojojin sun kuma mika wani daga cikin yan ta'ada da suka kama ga rundunar yan sanda
A wata sanarwa da kakakin rundunar ta kasa, Birgediya Janar Texas Chukwu ya fitar, rundunar da kama wani dan ta'adda kana sun mika shi ga rundunar yan sanda.
An kama wasu makamai da kayan alato tare dasu ciki har da babura 18 da bindigogi da harsashi da kunshin albarusai da adda daya.
Wannan ya biyo bayan arangama da yan sanda tare da hadin gwawar sojoji suka yi da wasu yan ta'adda a jihar Taraba.
Kamar yadda mataimakin kwamishnan yan sanda ta jihar, Faleye Olaleye, ya sanar, sunyi nasarar kashe yan tawaye 10 sakamakon arangamar tare da kama wasu makamai daga hannun su.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng