ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Sojoji sun kama wasu makiyaya 18

Kakakin ya bayyana cewa an mika wadanda aka kama ga hukumar yan sanda domin cigaban bincike kafin a gurfanar dasu gaban kotu domin zantar da hukunci

A wata takardar sanarwa da kakakin rundunar sojojin na kasa Birgediya janar Texas Chukwu, kakakin yace an kama wasu mabarnatan su shida yayin da suke cikin aikata laifin a yankin kwata suke kuma mutum biyu sun tsere yayin da dakaru ke sintiri a gundumomin Chembe, Tse-Gundu, Tse-Iordye da Sbaor  na jihar.

Makiyayan sun tsere daga kamuwa kana sun bar baburar su an kuma gano bindiga yayin yayin da sojojin ke safara.

Kakakin ya bayyana cewa an mika wadanda aka kama ga hukumar yan sanda domin cigaban bincike kafin a gurfanar dasu gaban kotu domin zantar da hukunci.

Birgediya Chukwu ya kuma sanar cewa an kama wasu makiyaya su 12 a gundumar  Mbayer/Yandez da Kaambee na jihar yayin da suke aiwatar da barna a gonakin jama'a.

ADVERTISEMENT

Rikicin jihar Benuwe

Jihar Benuwe ta sha fama da rikicin makiyaya da manoma wanda sakamakon rikicin an rasa rayukaa tare da salwantar dukiyoyi.

A ranar 5 ga wata mutum 24 sun rasa rayuka sakamakon harin da wasu da ake zargin cewa makiyaya ne suka kai garin Omusu Edimoga na karamar hukumar Okpokwu.

Lamarin ya biyo bayan binne mutum 73 da ri gwamnatin jihar tayi wadanda suka rasa rayukan su sakamakon rikicin da ya barke cikin 11 ga watan janairu na 2018.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT