Pulse.ng logo
Go

A jihar Taraba Sojoji sun kama dan leken asirin yan fashi

Wanda ake zargi ya amsa laifin taimakawa yan fashi wajen aiwatar da miyagun ayyuka a yankin.

  • Published:
Ayem Akpatuma: Troops arrest criminal informant in Taraba play

The suspect arrested by troops for being an informant for criminals in Taraba State

(Facebook/HQ Nigerian Army)

Sojojin nijeriya ta tabbatar da nasarar da tayi na kama wani gawurtaccen dan leken asriri a jihar Taraba yayin da yake kokari bada labari ga yan ta'adda.

A wata sanarwa da kakakin rundunar sojoji na kasa birgediya janar Texas Chukwu ya fitar ranar litinin 9 ga watan Afrilu, sojojin sun kama mai laifin ne yayin da yake kora bayanai kan waya ta yadda za'a kai ma wani hari.

Sanarwar tace bisa taimakon rahoton da aka sanar ma dakarun sojojin aka garkame mai laifin wanda ke shirin bada labarin kan yadda za'a kai ma wani hari a titin Takum zuwa Chanchangi dake jihar.

Wanda ake zargi ya amsa laifin taimakawa yan fashi  da suka addabi jama'a wajen aiwatar da miyagun ayyuka a yankin.

Domin kawo karshen matsalolin tsaro da ake fuskanta a kasar, rundunar ta kafa sabuwar shiri mai taken "Exercise Ayem Akpatuma" domin kawo karshen ta'adanci a jihohin Niger, Benue, Nasarawa, Taraba, Kogi da Kaduna.
 

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.