Pulse.ng logo
Go

Soja ya tafka barna Wani soja ya kashe matashi yayin da ake zanga-zanga

Matasan sun amince da shawarar da yan sanda suka basu na suka rubuta bukatun su kuma su tura ma kamfanin

  • Published:
ya harbi wani matashi yayin da suke zanga-zanga play

ya harbi wani matashi yayin da suke zanga-zanga

Wani matashi na garin Rumuji dake karamar hukumar Ekumua na jihar Ribas ya rasu sanadiyar harbin da soja dake kamfanin gidan mai na Greenvile yayi lokacin da suke zanga-zanga harabar kamfanin.

A rahoton da jaridar Punch ta fitar matasan garin sun kai koken su ga kamfanin inda suke kuka cewa kamfanin bata ba mutanen garin aiki yi kuma bata taimakawa wajen cigaban garin.

Rahoton ya bayyana cewa yayin da matasan ke zanga-zanga ne wasu sojoji da aka tura aiki a kamfanin suka yi harbi zuwa ga iska don su tsoratar da matasan.

Sanadiyar harbin ne wasu daga cikin matasan suka ji rauni har ma wani ya rasu cikin su.

A bisa bayanin rundunar yan sanda na garin Rumuji harbin da sojojin suka yi ya sami Chizam Nyache da Nna Aloha tare da wani wanda ba’a bayyana sunan shi yayin da suke zanga zanga.

Wani shugaban kungiyar matasan na garin Chikordi Orjim yace kamfanin taki tazo ayi bita kan sharudan tare da matakai da suka bi na siyan fili.

Orjim yayi barazana cewa matasan zasu cigaba da yin zanga-zanga indai ba’a biya bukatunsu.

Matasan sun amince da shawarar da yan sanda garin suka basu na su rubuta bukatun su kuma su tura ma kamfanin.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.