Hukumar yan sanda nijeriya sun zage damtse wajen tsaftace siyasa a Nijeriya musamman a jihar Kano inda zata fara daure yan siyasa masu ketara haddi.

Labarin haka ya fito ne daga bakin mai magana da yawun rundunar jihar Kano Magaji Musa Majiya yayin da ya gana da wakilin BBC a wajen taro kan tsaftace kalamai a gidajen rediyo.

Yana mai cewa "Magana ake ta siyasa yadda za ka baje hajarka ba tare da cin tumunci da zagin mutane ba. Haka ne ya sa muka soma taro da shugabannin kafafen watsa labarai da sojojin-baka da kuma hukumar da ke sa ido a kafafen watsa labara, wato NBC. Mun yi zube-ban-kwarya, don haka babu sani babu sabo ga duk wanda ya karya doka,".

Tashin hankali da siyasa ke haifarwa a jihar Kano

Jihar Kano tana daya daga cikin jihohi dake fuskanta zagon kasa daga yan siyasa da mabiyan su yayin taronsiyasa ko samun tsabani.

Sakamakon aika-aikar da yin haka ke haifarwa ba abun azo-a-gani bane domin mutane da dama sukan ji rauni kana wata sa'i a kan rasa rayuka.

Ko a kwanan baya hakan ya faru yayin da gwamnan jihar na yanzu da magajin sa suka shiga takun saka wanda har tsohon gwamna bai samu damar komawa jihar ba.

Mabiyan yan siyasan sun shiga halin kare jini biri a duk sanda suka ci karo da juna.

A cikin wani faifan bidiyon da yayi yawo a duniyar gizo, tsohon kwamishnan ayyuka ta mussaman wato Abdullahi  Abbas Sanusi yayi wasu kalaman tunzura wadanda ake zargin su suka haifi tarzomar tsakanin mabiyan akidojin.

Bisa ga wannan zargin kwamishnan yan sanda na jihar Kano ya tura ma kwamishnan tsammaci kan yazo ya bayyana dalilai da ya sanya ya furtar da kalaman.

Magoya bayan yan siyasan sun raunata junan su wanda sai da aka kafa kwamiti na musamman domin shawo kan yan siysan wajen kwantar da tashin hankalin da gabar su ke haifarwa.