Pulse.ng logo
Go

Bukola Saraki Shugaban majalisar dattawa ya yaba kokarin da kannywood keyi

Bukola Saraki ya kuma jinjina masu bisa gudummawar da suke bada wa na samad da aikin yi ga matasa a masana'antar.

  • Published:
Shugaban majalisar dattawa ya yaba kokarin da kannywood keyi play

Bukola Saraki ya amshi bakoncin jaruman kannywood

(Instagram/bukolasaraki)

Shugaban majalisar dattawa, Bukola Saraki ya jinjina ma masana'antar fim ta kannywood bisa rawar da take takawa wajen nishadantar al'umma.

Shugaban bayyana hakan ne bayan ya amshi bakoncin jaruman shirin "Mutum da addininsa" karkashin jagorancin Salisu Aliyu 'chal'.

 

Saraki yace yan wasan kannywood suna taka rawar gani wajen nishadantar da al'umma cikin yaren hausa.

Ya kuma jinjina masu bisa gudummawar da suke bada wa na samad da aikin yi ga matasa a masana'antar.

Shugaban majalisar dattawa ya yaba kokarin da kannywood keyi play (Instagram/bukolasaraki)

 

Salisu Aliyu wanda ya shirya fim din "Mutum da addininsa"ya jagorancin sauran jaruman shirin da suka hada da Ali Nuhu da Tijjani Faraga da Maryam Habila zuwa wajen Saraki.

Jaruman sun kai ma shugaban majalisar dattawa ziyarar ta musamman a ofishin sa dake Abuja.

 

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.