A bisa sanarwar da mai yi shugaban hidima kan kafofin sada zumunta Bashir Ahmad masu ruwa da tsakin sun tattauna da shugaban jiya talata 13 ga wata 2018.

Wannan ganawar ya biyo baya kwanan kadan bayan ganawar da shugaban yayi da Bola Tinubu. Sakamakon tattaunawar da suka yi, shugaba Buhari ya nada tsohon gwamnan jihar Legas a matsayin jagoran kwamitin neman sulhu tsakanin yan jam'iyar APC.

Tsohon gwamnan jihar Legas kuma jigon jam'iyar mai ci Bola Tinubu zai jagoranci wannan kwamitin neman sulhu domin magance rikici dake tsakanin yan jam'iya da ma shigabanin jama'a har da wasu dake rike da mukamai siyasa a jihohi daban daban na kasar.