Pulse.ng logo
Go

Bikin diyar gwamnan Kano Shugaban Hisba na Kano ya wanke kansa kan zargin da ake masa

Jama’a da dama na zargin hukumar ne da rashin adalci da tsoron fada ma gwamnati gaskiya duba da irin badala da aka yi a shagalin bikin Fatima Ganduje, wanda ake yi ma kallo da keta haddin musulunci da al’adar Hausa

  • Published:
Sheikh Aminu Daurawa play

Sheikh Aminu Daurawa

(hausaloaded.com)

Shugaban hukumar dake sa ido kan lamuran adinin musulunci na jihar Kano Sheikh Aminu ibrahim Daurawa ya wanke kansa kan zargin da jama'a keyi kan sa game da shurun da yayi game da badalar bikin diyar gwamnan Kano.

Bayan kusan sati daya da daura auren, shugaban hisba ya bada amsa kan dalilin da ya sanya ba'a ji daga gareshi kan batun bikin Fatima Gaduje da Idris Ajimobi.

Jama’a da dama na zargin hukumar ne da rashin adalci da tsoron fada ma gwamnati gaskiya duba da irin badala da aka yi a shagalin bikin Fatima Ganduje, wanda ake yi ma kallo da keta haddin musulunci da al’adar Hausa.

Fatima Ganduje da angon ta Idris Ajimobi play

Fatima Ganduje da angon ta Idris Ajimobi

(instagram/faaji2018)

 

*Sheikh Ahmad Gumi ya tsawatar kan badakalar bikin yar gidan gwamna

Sheikh Daurawa ya wanke kansa kan zargin da aka yi masa a shafin sa na facebook.

"A ranar Asabar  3 ga watan Maris Na tafi Sakkwato misalin karfe 1:00 an rana jim kadan bayan daura auren, domin halartar bitar littafin Dakta Mansur na Iziyya.

Bayan kwana biyu a Sakkwato na wuce jihar Zamfara domin yin wa'azi.

Na kwana daya a nan sannan na wuce zuwa jihar Kaduna domin halartar shirin sa'o'i biyu a gidan Talabijin na DITV. Ranar Juma'a na yi wa Mata wa'azi a Rigasa.

Daga baya sai na jagorancin hudubar Juma'a, bayan Sallar Magariba na yi Wa'azi a masallacin Sheikh Rabi'u Daura.

Ranar Asabar da safe na yi wa Mata Wa'azi a Masallacin Sultan Bello, daga nan na dawo jihar Kano. Ga duk wadanda suke son ganina na dawo ina ofis. Kowa na son jin me zan ce akan Shagalin auren 'yar GWAMNA, yanzu ku fada min me kuke so na fada?" ya rubuta a shafin sa na facebook.

Kan auren suma Wasu jaruman masana'antar Kannywood sun nuna bacin ran su kan rashin tsawatarwa daga malamai kan hoton diyar gwamnan jihar kano da angon ta dan gwamnan jihar Oyo.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement