ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Muhammadu Buhari yayi jimamin mutuwar AVM Muhammed

Shugaban yace Marigayi Mai kishin ƙasa ne kuma mutum mai kaunar ganin cigaban kasa

Shugaban kasa muhammadu Buhari ya siffanta marigayi Air vice Marshal Mukhtar Muhammed mai ritaya da mutum mai kishin ƙasa, mai ka’ida kuma daga cikin sojoji masu bin doka wanda ya sani kuma yana cikin mutane da yake girmamawa.

Shugaba Buhari ya bayyana haka a wata sakon ta’aziya da babban kakakin sa Garba Shehu ya fitar ranar litinin a garin Abuja.

Shugaban ya kara siffanta marigayi wanda yayi shugabancin jihar Kaduna a zamanin mulkin soja kuma shugaban gidan rediyo na freedom fm dake Kano a matsayin mutum mai kishin ƙasa kuma yana mai alfahari da cigaban ƙasa da ma yan ƙasar baki daya.

Shugaban ya tuna muhimmiyar rawar da tsohon jami’in rundunar sojojin sama ya taka wajen kafa jihar jihar Jigawa.

ADVERTISEMENT

Ya mika sakon ta’aziyar sa ga gwamnatain jihar, iyalin shi da al’ummar jihar Kano game da wannan babban rashi da suka samu.

Shugaba Buhari yayi ma marigayi fatan Allah ya jikan shi da rahama.

Marigayi Mukhtar Muhammed wanda ya rike sarautar “wazirin Dutse” ya rasu rana lahadi a asibiti dake birnin London bayan jinya da yayi.

Shine gwamnan Jihar Kaduna na farko bayan an kafa ta a matasayin jiha a 1977 a karkashin  mulkin soja na Olusegun Obasanjo.

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT