Pulse.ng logo
Go

Yanzu-yanzu Shugaba Buhari yana ganawan sirri da jagororin majalisar dattawa

Ganawar yana gudana a fadar shugaban dake nan Villa

  • Published:
Shugaba Buhari tare da shugaban majalisa dattawa da kakakin majalisar wakilai play

Shugaba Buhari tare da shugaban majalisa dattawa da kakakin majalisar wakilai

(Instagram/Buharisallau)

Bayan gayatar da majalisa tayi masa kwanan baya, shugaban kasa Muhammadu Buhari yana ganawar sirri da jagororin majalisar tarayya.

Ganawar tasu yana gudana ne a fadar shugaban dake nan Villa.

Kamar yadda hadimion sa Bashir Ahmad ya sanar, shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kakakin majalisar wakilai, Yakubu Dogara sun gana da shugaban ne kan bayanan kazafin kudin 2018.

Shugaban ya gana da su ne sa'o' i kadan bayan dawowar shi daga mahaifar sa, inda ya gudanar da zaben jagororin jam'iyar APC na jihohin wanda aka gudanar a ranar hutun mako.

A makon da ya gabata, majalisar wakilai ta bukaci shugaban da ya gabata gaban ta domin bada amsar tambayoyin game da kashe-kashen dake faruwa a kasar.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.