Pulse.ng logo
Go

Mutuwar Sheikh Imam Lawal Shugaba Buhari ya taya jihar sa jimamin mutuwar babban limami

Babban malamin ya rasu ne a safiyar ranar Lahadi 6 ga watan Mayu, a gidan sa dake nan unguwar Liman na garin Katsina. Anyi jana'izar shi karfe 2:30 na rana

  • Published:
Shugaba Muhammadu Buhari play

Shugaba Muhammadu Buhari

(Nigerian tribune)

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya gwamnatin jihar Katsina da al'ummar ta jimamin mutuwar limamin babbar masallaci jihar, Sheikh Imam Lawal.

Babban malamin ya rasu ne a safiyar ranar Lahadi 6 ga watan Mayu, a gidan sa dake nan unguwar Liman na garin Katsina. Anyi jana'izar shi karfe 2:30 na rana.

Marigayi, Sheikh Imam Lawal play

Marigayi, Sheikh Imam Lawal

(Facebook/rariya)

 

A wata takardar sanarwa da kakakin shugaban Garba Shehu ya sa hannu, shugaban ya taya iyalan marigayi da sauran al'ummar jihar juyayin mutuwar sa.

Kamar yadda takardar ta bayyanar, Shugaban ya yaba halayen marigayin bisa yadda ya tafiyar da rayuwar sa wajen raya addinin musulunci.

yayi kira ga jama'a da a yi koyi da kyakkywar halin  sa na zama tare da mutane cikin soyayya da zaman lafiya da kyakkyawar zamantakewa da makwabta da sauran jama'a.

Daga shugaban, ya yi ma marigayin addu'ar Allah ya jikan shi da rahama tare da yi iyalen sa addu'ar Allah ya basu hakurin jure rashin sa.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.