ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Shugaba Buhari ya sa hannu ga takarda kan kudirin baiwa matasa damar tsayawa takara

Shugaban ya cika alkawarin da ya dauka yayin da yake jawabi na raya ranar dimokradiya inda ya bayyana cewa zai sa hannu ga wannan dokar nan bada dadewa ba.

Shugaban ya cika alkawarin da ya dauka yayin da yake jawabi na murnar zagayowar ranar dimokradiya inda ya bayyana cewa zai sa hannu ga wannan dokar nan bada dadewa ba.

Yayin hakan ne kafin zaman majalisar sa da aka saba yi ko wace sati a fadar sa dake nan Abuja.

Tun a cikin watan yuli na 2017 majalisar tarayya ta amince da kudirin kafin ta tura ga shugaban domin ya tabbatar da ita kana yasa sa hannu.

ADVERTISEMENT

Bisa ga wannan sabuwar canji, dokar zai baiwa matasa masu shekaru 35 damar tsayawa takarar kujerar shugaban kasa a maimakon shekara 40.

Hakazalika masu shekaru 30 zasu iya tsayawa takarar kujerar gwamna da majalisar dattawa.

Har ila yau dai yan shekaru 25 suma zasu iya tsayawa takarar majalisar wakilai ta jiha da na tarayya.

Kungiyar dake fafitikar wajen gani an dama da matasa a harkar siyasa ta YIAGA tayi farin ciki bisa wannan sabuwar canji da aka samu a kundin tsarin mulkin kasa.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT