Pulse.ng logo
Go

Labari cikin hotuna Shugaba Buhari ya mika tambarin yabo ga iyalen Abiola da Fawehinmi

An gudanar da bikin a dakin taro dake fadar shugaban a garin Abuja ranar Talata 12 ga watan Yuni

  • Published:
Kola Abiola ya amshi kyautar a madadin iyayen marigayi play

Kola Abiola ya amshi kyautar a madadin iyayen marigayi

(Instagram/buharisallau)

Shugaban kasa Muhammadu buhari ya mika takardar lambar yabo ga iyalen marigayin Alhaji Moshood Abiola da Gani Fawehinmi.

Shugaban yayi hakan ne a garin Abuja ranar talata a bikin karrama yan gwaggwarmayar siyasa da aka shirya a fadar sa.

Shugaba Buhari yayin da yake mika kyuata ga uwargidan marigayi Gani Fawehinmi play

Shugaba Buhari yayin da yake mika kyuata ga uwargidan marigayi Gani Fawehinmi

(Instagram/buharisallau)

 

Tun a cikin ranar 6 ga watan yuni shugaban ya sanar cewa zai karrama marigayin bayan ya sauya ranar bikin dimokradiya daga watan Mayu zuwa 12 ga watan Yuni mutunta gwaggwarmaya da aka yi a zaben 1993.

Manyan yan kasa masu hannu da shuni sun halarci taron karramawa da aka shirya a fadar shugaban kasa play

Manyan yan kasa masu hannu da shuni sun halarci taron karramawa da aka shirya a fadar shugaban kasa

(Instagram/buharisallau)

Ya karrama tsohon dan takarar kujeran shugaban kasa wanda ake kyuatata zato shi ya lashe zaben da darajar GCFR.

Babban dan dan marigayin Kola Abiola, ya amshi kyautar a madadin sauran iyalen.

Bayan ga haka shugaban ya karrama Baba Gana Kingibe wanda ya tsaya a matsayin mataimakin Abiola da darajar GCON.

play (Instagram/buharisallau)

A bikin raya wannan kyaututuka, manyan jami'an gwamnati da sauran jama'a masu hannu da shuni a fannoni daban daban sun halarci taron.

Wani abun birgewa da ya faru a wajen taron bikin shine, yadda shugaban kasa ya mutunta matar marigayi Gani Fawehinmi.

play (Instagram/buharisallau)

 

Yadda hotuna suka bayyana, shugaban ya durkasa domin daukar wani abu da ya fado daga hannun ta duk da cewa sakataren gwamnatin tarayya ya yunkurin wajen daukan abun gabanin shugaban.

Hoton lamarin yayi musababbin abun muhawara a kafafen sada zumunta inda wasu da dama suka yaba abun da shugaban yayi.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.