ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Martanin Shugaba Buhari ga Obasanjo da Atiku

Ranar Alhamis 11 ga wata ne dan takarar jam'iyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya kai a tsohon ubangidan sa ziyara a gidansa dake garin Ota inda a nan ne Obasanjo ya bayyana cewa zai goya masa baya a zaben 2019.

Wani majiya ya shaida mana cewa ganawar da jiga-jigan suka yi zata kulla kyakkyawar alaka tsakanin tsofafin abokan hammaya kuma ana kyautata zato cewa Obasanjo zai bude kofar sa na mara ma Atiku baya a zaben 2019 domin kayar da anniyar shugaba Buhari na zarcewa a saman kujerar mulkin Nijeriya.

Martanin fadar shugaban kasa

A cikin sanarwa da hadimin Shugaba Buhari kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu ya wallafa a shafinsa na Twitter, ya ce ba su yi mamakin labarin da ke cewa Obasanjo yana goyon bayan Atiku a zaben 2019 dmin dukansu ba za su yi nasara ba.

"Ba mu manta ba kuma 'yan Najeriya su ma suna sane cewa kimanin shekara 11 da ta wuce ne tsohon shugaban da kuma tsohon mataimakinsa a kokarinsu na neman mulki suka zargi juna da aikata cin hanci da karbar rashawa," in ji Malam Garba Shehu.

ADVERTISEMENT

Kamar yadda rahotanni suka bayyana , Atiku ya isa zauren gidan Obasanjo a daidai karfe 1:05 na rana tare da wasu jiga-jigan PDP da wasu manyan malaman addini.

Cikin tawagar da suka garzaya gidan tsohon shugaban kasa akwai shugaban jam'iyar PDP, Uche Secondus, jagoran kungiyar Afenifere, cif Ayo Adebanjo, shugaban yakin neman zaben Atiku, Gbenga Daniel da Sanata Ben Murray-Bruce.

A bangaren malamai kuwa akwai Bishop Mathew Kukah, Bishop David Oyedepo da kuma Sheikh Ahmad Gummi.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT