Pulse.ng logo
Go

Fadar shugaban kasa Shugaba Buhari ya karbi fom din takarar sa

Bayan kwana biyu da siyan fom din kungiyar Nigerian Consolidation Ambassadors Network ta mika takardar ga shugaba Buhari.

  • Published:
Over 70 candidates to contest against Buhari in 2019 election play Shugaba yayi ma kungiyar godiya (Twitter/@BashirAhmaad)

Shugaba Muhammadu Buhari yayi ido hudu da fom din tsayawa takara da aka siya mashi a kan N45M.

Kungiyar Nigerian Consolidation Ambassadors Network  karkashin jagorancin shugaban ta Alhaji Sanusi Musa ta mika ma shugaban fom din a fadar sa ranar Talata 11 ga watan Satumba.

A ranar 5 ga wata kungiyar ta siya takardar tsayawa takarar shugaban domin ya zarce da mulkin kasa bayan sun nuna gamsuwar su ga shugabancin sa.

PDP condemns Buhari for receiving N45m nomination form from group play A ranar 5 ga watan Satumba kungiyar ta siya ma shugaban fom din neman takara (Presidency )

 

A jawabin sa yayin da ya karbin tawagar kungiyar, shugaba Buhari yayi masu godiya bisa yarda da suka yi masa.

Jim kadan bayan jam'iyar APC ta fitar da kudaden neman takarar ta gabatar da kudin neman takarar shugaban.

Buying nomination forms for rich politicians makes no sense whatsoever play Shugaban ya karbi bakoncin kungiyar a fadar sa ranar 11 ga watan Satumba (Presidency )

 

Ta mika takardar miliyan arba'in da biyar ga shugaban jam'iyar Adams Oshiomole.

Sanusi ya shaida cewa ya'yan kungiyar tunda daga karkara da kananan hukumomi na jihohin kasa suka hada kudin siyan takardar domin nuna gamsuwar su ga shugabancin shugaba Buhari.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement