Manyan jiga-jigan masanaantar fina-finan da wakokin hausa ta Kannywood sun ziyarci fadar shugaban kasa domin yin liyafa da shugaba Muhammadu Buhari.

Fadar shugaban dake Abuja ta karbi bakoncin yan wasan daren ranar Alhamis 18 ga watan Oktoba 2018.

Tawagar yan wasan da suka halarci liyafar tare da shugaban sun hada da shugabanni masu rike da muhimman mukamai a Kannywood tare da jarumai maza da mata da mawaka tare da manyan masu shirya fina-finai da masu bada umarni.

Cikin manyan bakin da suka halarci liyafar da shugaban ya shirya ma yan wasan sun hada da gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-rufai, Gwamnan jihar Filato, Simon Lalong da dan majalisar wakilai na tarayya, Honarabul Nasir Ali Ahmed.

A bangaren ma'aikatan fadar shugaban kasa akwai shugaban ma'aikatan fadar, Mallam Abba Kyari, Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha sai hadimin shugaban a bangaren yadda labarai na kafafen sada zumunta, Bashir Ahmad.

Yan kannywood sun nuna goyon bayan su ga shugaban na zarcewaa saman kujerar  shugabancin kasa a zaben 2019.

Yayin da yake jawabi wajen liyafar, Nura Hussein ya jaddada cewa "2019 Ba kudi ba, sai dai a danna mu a yanke. Zamu dangwala maka da jinnin mu,".

Fadar shugaban tayi ma yan wasan alkawarin wajen yaki tare da kawo karshen masu satar fasaha wanda ke gurgunta alamuran masana'antar nishadi.

Tun ba yau ba wasu daga cikin fitattun jaruman suke nuna goyon bayan su ga dan takarar APC a zaben dake gabatowa.

Wasu daga cikin su sun wallafa hotuna tare da fitar da wakoki domin tabbatar da matsayin su ga shugaban gabanin zaben.