Kakakin shugaban Femi Adeshina ya sanar da haka ga manema labarai. A takardan da kakakin ya fitar, shugaban zai halarci taron wanda za'a gudanar a Abidjan babban birnin kasar Cote d'ivoire tsakanin ranar 28 da 29 na watan yau.
Shugaba Buhari na shirin barin kasar zuwa Cote d'ivoire
Shugaban zai halarci taron gamayar majalisar kasashen afrika da ta turai a Abidjan
A kwanan baya shugaban ya halarci taron ECOWAS a kasar jomhoriyar Nijar inda aka tattauna kan amfani da kudi bai daya tsakanin kasashen dake cikin ECOWAS.
Taken taron shine "Zuba jari ga matasa domin samad da tabbataciyar cigaba" kuma shugaba Buhari zaiyi amfanin da damar wajen ganawa da sauran shugabannin kasashen afrika da ma na kasashen turai.
Karanta labarin>>Bayan ziyarar da yakai yankin kudancin kasa, shugaba Buhari ya dawo gida da abun farin ciki
Cikin tawagar shugaban wadanda zasu raka shi taron akwai gwamnan jihar akwa ibom Udom Emmanuel da takwaran sa na jihar Bauchi Alhaji Muhammed Abubakar tare da wasu yan majalisar shugaban.
JOIN OUR PULSE COMMUNITY!
Eyewitness? Submit your stories now via social or:
Email: eyewitness@pulse.ng