ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Auren da gwamna da minista da shugabannin kasa ke zuwa haram suke yi- Sheikh Gummi ya tsokaci game da auren yaran gwamnoni

Malamin ya soki shugabanni tare da yi masu gargadi kan fifice alamuran ul'ummar da suke shugabanta fiye da yin badakalar da kudin jama'a kan abun mara tasiri.

Malamin ya gargadin shugabanin kan mayar da hankali wajen aiwatar da ayyukan da zai amfani al'ummar da suke shugabanta fiye da zuwa inda bai kamata ba tare da barnata kudin jama'a wajen yin haka.

Yayi hakan ne a karatun sa na fassarar litafin Muwata malik wanda yake gudanarwa ko wace sati a masallacin sultan Bello dake nan garin Kaduna.

Sheikh Gummi ya gargadi shugabannin wajen kaurace aikata haram da barnata kudin jama'a kan zuwa ire-iren bukukuwan aure a maimakon su zauna tare da al'ummar da suke shugabanta.

ADVERTISEMENT

Malamin ya bada misalin faruwar irin haka a lokacin gwamnatin da inda tsohon shugaban kasa ya aurar da diyar shi wanda a lokacin ya samu halartar manya manya masu ruwa da tsaki ciki har da gwamnoni duk da cewa a lokacin yankin tana fuskantar barazar yan ta'addar boko domin ana samun tashe-tashen bama-bamai amma wannan bai hana shugabannin halartar daurin aure.

A cewar sa yayi masu gargadi kan badakalar kudin jama'a da kuma kayyade ranar haduwa da sauran shugabannin a ire-iren wannan ranar.

Ba tare da nuna alaka ga siyasa, babban malamin yana mai cewa ya zama dole yayi gargadi ga faruwar hakan tunda yayi makamancin hakan ga gwamnatin baya.

Labarin auren Fatima Ganduje da Idris Ajimobi yayi yawo a kafafen sada zumunta inda ake ta yadda hotunan shagulgulan biki da aka gudanar don raya daurin auren su.

Malamin dai yayi Allah-wadai kan hoton ma'auratar da yayi yawo inda mijin ya rungumi amaryarshi ga bainar duniya tare da nuna fasikanci fili.

ADVERTISEMENT

Yace ma'auratan sun kasance a abun koyi ga al'umma bai kamata ire-iren hotuna suna yawo ga idon jama'a.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT