Pulse.ng logo
Go

Maulidin Sheikh Ibrahim Inyass Sheikh Dahiru Bauchi ya kalubalanci yan darikar Tijjaniya kan katin zabe

Babban malamin ya kalubalanci yan darikar tijjaniya da suyi gaggawa wajen mallakar katin zabe domin ita ce makami da zai taimaka wajen zaben shugabanni mafi soyuwa a garesu kuma wadanda zasu kawo sauyi da cigaba

  • Published: , Refreshed:
Sheikh Dahiru Usman Bauchi play

Sheikh Dahiru Usman Bauchi

(Daily Trust)

Jagoran darikar tijjaniya Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya kalubalanci mabiyan akidar sa wajen samun katin zabe yayin da zabe ke gabatowa.

Shahararren malamin yayi wannan kiran a wajen taron maulidin Sheikh Ibrahim Inyass karo na 42 wanda ake gudanarwa ko wani shekara wanda aka gudanar a garin abuja ranar asabar 14 ga watan Afrilu.

A bisa bayanin sa, babban malamin ya kalubalanci yan darikar tijjaniya da suyi gaggawa wajen mallakar katin zabe domin ita ce makami da zai taimaka wajen zaben shugabanni mafi soyuwa a garesu kuma wadanda zasu kawo sauyi da cigaba.

Ya kuma kira da ayi amfanin da katin wajen zaben shugabannin managarta masu kishin kasa kuma wadanda zasu biya bukatun jama'a da suke shugabanta.

Malamin yayi karin haske kan taron maulidi na bana inda yake cewa, makasudin taron shine don karrama fiyeyyen malami Sheikh Ibrahim Inyass bisa gudummawar da ya bayar ga addinin musulunci a Afrika, Asiya da ma duniyar baki daya.

Ya kara da cewa yan darikar tijjaniya sunyi amfani da wannan bikin maulidin wajen yima kasa adduar zaman lafiya da kuma samun mafita kan matsalolin da kasar ke fama da ita.

Bayanan shugaban kasa a taron

Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana cewa Ibrahim Inyass ya taka muhimiyar rawa wajen  cigaban addinin musulunci a duniya.

Shugaban wanda ministan ilimi Adamu Adamu ya wakilta a wajen taron ya jaddada cewa gwamnatin tarayya zata cigaban da taimakawa tafiyar yan darika da yakinin samad da zaman lafiya a kasa.

Yayi kira ga jagorori da mabiyan darikar tijjaniya da su dukufa wajen yi ma kasa addua wajen samun cigaba.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.