Pulse.ng logo
Go

Shehu Sani Dalilin da ya sa na fallasa kudin da muke karba

Ya kara da cewa sama da shekara 19 kenan da ake zargin 'yan majalisar da karbar miliyoyin kudi, amma kuma sun kasa fitowa su kare kansu., su kuma yi wa 'yan Najeriya bayanin ainahin kudaden da suke dauka a matsayin albashi ko na alawus.

  • Published:
Shehu Sani urges APC to drop idea of indirect primaries play

Senator Shehu Sani

(Guardian Nigeria )

Dan majalisar dattawa wanda ya fallasa adadin kudin da suke amsa yayi karin haske kan dalilin da ya sa ya fallasa kudin da yan majalisar ke amsa ko wani wata.

A makon da ya gabata ne dan majalisar ya bayyana hakan yayin da zanta da jaridar Thenews.

Shehu Sani sanar cewa ko wani sanata yana amsar N13.5M ko wani wata kana suna amsar N200M domin gudanar da ayyuka a mazabar su.

Duk da wannan kudin ana kuma basu albashin N750,000.

Hirar shi da wakilin BBC sanatan yace ya tona asiri ba tare da manufar tozarta yan majalisar sai dai yayi hakan ne don kawar da zargin da ake masu na mara gaskiya masu boye kudin da suke amsa.

Ya kara da cewa sama da shekara 19 kenan da ake zargin 'yan majalisar da karbar miliyoyin kudi, amma kuma sun kasa fitowa su kare kansu., su kuma yi wa 'yan Najeriya bayanin ainahin kudaden da suke dauka a matsayin albashi ko na alawus.

Yace wata manufa dake tare da yin haka shine domin sauran bangarorin gwamnatin suma su bayyana adadin kudin da suke samu tare da aikin da suke dasu. kama daga alkalai, ministoci, gwamnoni da sauran masu ruwa da tsaki a hukumomin gwamnati.

"Ba wai shekara uku da ya yi a matsayin Sanata ba ake magana, abun lura shi ne sama da shekara 19 kenan ana kan wannan turbar, kuma daruruwan mutane sun yi aikin majalisar sun tafi, wasu kuma za su zo."  yace.

Yace mutane na gudun abun da zai faru bayan bayyana hakan shiyasa ba'a fallasa ba tun shekarun baya.

"Saboda haka ko ma a wanne lokaci ka fadi gaskiya, ka dai fade ta, kuma abin da ya sa mutane suke gudun fadar gaskiya shi ne gudun abin da zai same su.''

Sanatan yace bai san ko majalisar zata dauki mataki kan tonon asirin da yayi.

Do you ever witness news or have a story that should be featured on Pulse Nigeria?
Submit your stories, pictures and videos to us now via WhatsApp: +2349055172167, Social Media @pulsenigeria247: #PulseEyewitness & DM or Email: eyewitness@pulse.ng. More information here.

X
Advertisement