ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Wani ya rasu sanadiyar bulala da aka yi mai a jihar Katsina

Inusa ya zane Saidu ba tare da an samu cikas amma da abun ya zagayo ga Saidu wakar ta canja

An samu labarin rasuwar wani matashi sanadiyar bulala da aka yi mai yayin da suke gasar neman aure a jihar Katsina.

Bisa rahoto da jaridar Punch ta fitar gasar ya faru tsakani wasu yan fulani Yari Inusa da Saidu

Yari Inusa ya rasu sanadiyar bulala da aka yi mai a gasar neman aure wanda aka fi sani da Sharo a al’adar Fulani.

Lamarin ya faru ne a kauyen Durmin Biri dake karamar hukumar Kafur dake jihar Katsina.

ADVERTISEMENT

Hukumar yan sanda ta sanr cewa Inuwa ya rasu bayan rauni da ya samu a kan shi bayan bugun da Saidu yayi mai a gasar Sharo da suka yi.

Inusa ya zane Saidu ba tare da an samu cikas amma da abun ya zagayo ga Saidu wakar ta canja yayin da ya zane shi a kai a maimakon bayan shi.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar yan sanda dake jihar Katsina DSP Gambo Isah ya tabbatar da haka.

Ya sanar cewa mahaifin Inusa ya kai kara ga yan sanda wanda yayi sanadiyar kama Saidu.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT