ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT

Hotunan shagalin bikin auren Fatima Dangote da Jamil Abubakar a Legas

Bill Gates, Aisha Buhari, Yemi Osinbajo da uwargidan sa tare da sauran jiga-jigan harkar siyasa da kasuwanci sun halarci taron wanda aka gudanar a dakin taro na Eko Hotel

Bikin wanda aka gudanar a dakin taro na Eko Hotel ya samu halartar manyan baki masu hannu da shuni a fannoni daban daban.

An daura auren Jamil Abubakar da amaryar sa Fatima Dangotea fadar sarkin Kano ranar 16 ga watan Maris wanda ya samu halartar shugaban kasaMuhammadu Buhari a matsayin babban bako.

Kamar yadda rahotanni suka zo mana, shirye shiryen kafin bikin ya janyo cinkoso a yankin Victoria island inda dakin taron yake.

Bikin ya gudana ne bayan wadanda aka gudanar a garin Kaduna (Garin mahaifiyar amarya) da Kano inda aka daura auren su da kuma wanda aka gudanar a Abuja.

ADVERTISEMENT

Attajiri na biyu mafi arziki a duniya Bill Gates ya halarci taron tare da wasu manyan yan kasuwa na Nijeriya da kewaye.

Hakazalika shugaban kasa Ghana Nana Akufo Ado da sarkin Kano Mai martaba Muhammad Sanusi na biyu tare tsohon shugaban kasar jamhoriyar Benin Boni Yayi sun raya daren tare da iyayen ma'auratan.

Uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari da mataimakin shugaban Yemi Osinbajo da matar Dolapo Osinbajo sun halarci taron bikin.

Tsofafin shugabannin kasa Yakubu Gowon da Olusegun Obasanjo da shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da kakakin majalisar Yakubu Dogara suma sun hallara.

Fitattun mawakan nijeriya Wizkid, Davido da Phyno sun nishadantar da baki.

ADVERTISEMENT

Banda yan siyasa, suma manya masu ruwa da tsaki a masana'antar nishadantarwa da kafafen watsa labarai ba'a baro su baya ba.

Enhance Your Pulse News Experience!

Get rewards worth up to $20 when selected to participate in our exclusive focus group. Your input will help us to make informed decisions that align with your needs and preferences.

I've got feedback!

JOIN OUR PULSE COMMUNITY!

Unblock notifications in browser settings.
ADVERTISEMENT

Eyewitness? Submit your stories now via social or:

Email: eyewitness@pulse.ng

ADVERTISEMENT
ADVERTISEMENT